A yammacin ranar lahadin data gabata ne da misalin karfe 3:00 na rana wasu mutane uku sun harbi wani matashi mai suna jamilu iliyasu mai sana’ar saida fulawowin adon gida a unguwar dorayi karshen waya dake karamar hukumar kumbotso.
Daga wakilin aksammedia B.imam
Matashin dai ya bayyana mana cewar ya samu kira kira daga wani abokin huldar sa na kasuwanci da misalin karfe 1:00 na rana inda ya kirashi da yazo domin su kulla abinda suka saba zuwan sa keda wuya yayi ido biyu da wadannan mutane su hudu hadda abokin huldar tasa daya ambata shar sai suka shara masa mari madi da harbinsa a kafar sa tare da ambata masa cewar iyya motsa zasu harbe shi a kirjin sa.
Wani matashi mai saida katin haraji na yan adaidaita sahu mai suna aliyu musa ya tabbatar da faruwar lamarin da cewar yaga mutumin da sukai awan gaba dashi da bakar mota ya ajiye jim kadan sai ga mutane uku sun shiga harabar wannan wajan saida fulawoyin bayan sun kammala aika aikar tasu sai suka saka wannan magidanci a mota sukai hanyar kofar famfo.