Kwamitin Bincike na Majalisar Wakilai a kasar Amurka, tun ranar 6 ga watan Janairu ta gayyaci tsohon shugaban kasar, Donald Trump domin amsa wasu tambayoyi.
A kuri’ar da aka kada a zaman Kwamitin Majalisar Wakilai na musamman da aka kafa domin gudanar da bincike kan harin da aka kai ginin majalisar na ranar 6 ga watan Janairun 2021 a kasar, dukkan mambobi 9 sun kada kuri’ar amincewa kan kudirin gayyatar Donald Trump don ba da jawabi.
Shugaban kwamitin, Bennie Thompson ya bayar da sanarwa bayan kada kuri’ar, inda ya ce, “Trump shine mutumin da ke tsakiyar lamarin da ya afku a ranar 6 ga watan Janairu. Shi ya sa muke son jin ta bakinsa.”
Thompson ya ce ya kamata kwamitin ya saurari abubuwan da suka faru a ranar 6 ga watan Janairu gaba daya.
Bayan Joe Biden ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar a ranar 3 ga watan Nuwamban 2020, magoya bayan Donald Trump, wadanda ba su amince da sakamakon zaben ba, sun kai hari kan harabar majalisar a ranar 6 ga watan Janairu, yayin da mutane 5 suka mutu a rikicn da ya barke.
Tare da ikirarinsa cewa rashin nasarar da ya yi a zaben da Joe Biden ya samo asali ne sakamakon zamba da kuma yin karya ga jama’a, an zarge Trump da ingiza ‘yan tawayen da tayar da tarzoma a wani yunkuri na ganin cewa an soke zaben.