Daga Walid Hari.
Wannan shi ne karo na 66 da za a gudanar da bikin, wanda za a yi a Faransa, don fayyace gwarzon dan kwallon kafa na kakar 2021/22.
A karon farko a tarihin Ballon d’Or za a bayyana gwarzo bisa kwazonsa a kakar tamaula, maimakon shekara daya.
Lionel Messi mai rike da kyautar bara baya cikin ‘yan takara, kuma a karon farko a shekara 17 da ba sunan kyaftin din Argentina
Tun daga 2008 Messi da Cristiano Ronaldo ke bani in baka wajen lashe kyautar ballon d’Or, in banda 2018 da Luka Modric ya zama zakara.
To sai dai kuma a bana masana na ganin ba wanda ya kamata ya lashe kyautar fiye da dan kwallon tawagar Faransa da Real Madrid, Karim Benzema.
Dan wasan shi ne ya dauki La Liga a bara da Champions League, kuma shi ne kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da ta zakarun Turai.