Wani hatsarin Mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama,inda wasu Kuma suka hadu da munanan raunika.
Hatsarin dai ya afku ne a yadakwari dake yankin karamar hukumar Kura, inda wata babbar motar daukar dakon Mai talakume wasu motoci guda biyu Wanda da ke cike tab da mutane.
Akalla ba a kasara ba kimanin mutane biyar ne suka rigamu zuwa gidan gaskiya inda wasu Kuma suka jikkata.
jamian hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa reshan jahar kano sun garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti Dan basu agajin gaggawa.
Shedan gani da ido ya bayyanawa majiyar mu cewa tayar babbar motar ce ta gaba ta fashe Hakan yasa motar ta lakume motocin da dama.