Ƙungiyoyin kasa da kasa dake sa ido kan zaɓe na IRI da NDI sun bayyana muhimmancin yin sahihin zaɓe a Najeriya musamman babban zaɓen dubu biyu da ashirin da uku dake ƙaratowa.
Kungiyoyin sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a babban Birnin tarayya Abuja, inda suka ce Najeriya na kan hanyar aiwatar da sahihin zaɓe, amma akasin hakan ka iya sa yan kasar su daina kaɗa kuri’u a zabuka gaba daya.
Kasancewar Najeriya a matsayin ƙasa mafi muhimmanci a nahiyar Afirka kuma wacce ta fi kowacce a fannin dimokaradiyya hakan ya sa kungiyoyin ƙasa da ƙasa dama hukumomin ƙasashe duniya ke sanya ido a irin wannan lokaci da zaɓen ke ƙaratowa.
Wannan daliline yasa kungiyoyin sa ido kan harkokin zabe na international Republic institute da national democratic institute suka hada wannan taron manema labarai don bayyana irin binciken da su ka yi kan shirye-shiryen zaben baɗi.
Idan Aka Kasa Yin Sahihin Zaɓe A 2023 ‘Ƴan Najeriya Na Iya Daina Kada Kuri’a A Zabuka – Kungiyoyin Sa Ido Kan Zabe
Yayin jawabi a gurin taron Dr. Christopher Fomunyoh ya bayyana cewa zaɓen na baɗi na da muhimmanci ga Najeriya musamman yadda aka sami fitowar yan takara masu karfi.
Ya ce fitowar tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da Tsohon gwamnan Anambra Peter obi ya kara wa harkar zaben armashi da kuma gasa tsakanin jam’iyyu wanda zai iya sawa a kasa samun wanda ya ci zabe sai an koma zagaye na biyu wanda zai zama na farko a tarihin dimokaradiyyar Najeriya. ya kara da cewa Sahihin zaɓe abu ne mai muhimmanci wanda da alama Najeriya na kan turbar hakan, amma hanzari ba gudu ba idan aka sami akasin hakan yan Najeriya na iya daina kada kuri’a a zabuka.
A nata jawabin mataimakiyar darakta mai kula da nahiyar Afrika a kungiyar IRI Jenai Cox tace yadda aka tsawwala kudin neman tsayawa takara ya hana mutane da dama da suka dace shiga a dama dasu