Anyi kira ga gwamnatin jihar Kano kan ta cigaba da jaddada shirinta na koyawa matasa sanaoi domin su dogara da kansu a fadin jihar nan.
Shugaban kwamitin amintattu na kasuwar wayoyin hannu dake jihar nan Alhaji Abdullahi wanda aka fi sani da Abdul Gama ne ya yi wannan kiran a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Alhaji Abdul Gama Ya bayyana cewar daga cikin matasa miliyan uku dake jihar nan kimanin miliyan daya ne ke gudanar da harkar sanaar wayoyin hannu a jihar Kano.
Ya kuma bayyana cewar idan har gwamnati ta dore da koyawa matasa sanaoi tare da bibiyar shirin ta yadda zai amfane su to lallai zaa rage yawan samun batagari a fadin jihar.
Abdul Gama ya kuma koka dangane da Karin farashin man fetur da kuma hauhawar farashin dala da yen na kasar China inda yace kasuwancin mafi akasarin yan kasuwar su ya dakata sakamakon hauhawar farashin.
Ya kara da cewar karuwar farashin dala da yen Ya karu ta yadda idan zaka yi safarar kaya zuwa kasarnan Sai ka rubanya kudinsa da kake kashewa a baya kafin ka sayi kayan Wanda hakan yayi sanadiyar durkusar da kasuwancin yan kasuwa dake jihar nan.
Ya kuma bayyana cewar wannan Karin shine yake tilasta su su kara farashin kayayyakin su daga lokaci zuwa lokaci Wanda daga karshe hauhawar farashin kan masu saye yake fadawa.
Don haka yake kira ga gwamnati kan ta shiga lamarin wannan hauhawar farashin dala da yen don ceto yan kasuwar su daga karyewa tare da durkushewar tattalin arzikin jihar nan.
Kazalika Abdul Gama ya kuma yi Kira ga gwamnatin tarayya kan ta yi duk maiyiwuwa wajen ganin ta waiwayi jihohin dake da man fetur musamman ma a Arewacin kasarnan domin hako shi ta yadda zai wadata har ma farashin sa yayi sauki kasancewar Najeriya na daya daga cikin kasashen da man fetur din su yake da kyau a duniya.
Daga karshe yayi kira ga matasan jiharnan kan su tabbata sun mallaki katin zabe saboda shi ne kadai hanyar da Zasu iya sauya gwamnati ta hanyar zaben shugabanni nagari a kasarnan.