Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa ta jaddada kudirin ta na yin aiki bisa gaskiya da rikon amana a fadin kasan nan .
Babban Jami’i mai kula da rundunar dake iyakar Najeriya da Kasar Nijar ta Illela cikin jihar Sakkwato Mr Victor Nwokile, ne ya tabbatar da haka.
Nwokile da yake jawabi a bikin mako daya da ya gudana domin masu hurda da hukumar ya bayyana gaskiya a matsayinsa abin da ya Dace kowanna maaikaci ya rike ta domin inganta aikin sa domin gyara da tserar da rayuwar su.