Matasa da dama a jam’iyar APC na nuna muradun su na ganin lokaci yayi da yaro matashi Mai matsakaitan shekaru zai jagoranci jam’yar a making kasa.
Hakan na zuwane a daidai lokacin da wasu jagororin kungiyoyin matasa a jam’iyar APC suka ziyarci matashi Mai shaawar tsayawa takarar, Alh Nasiru Saleh M Gashuwa.
Da yake jawabi M Gashuwa yace akwai bukatar a rika damawa da matasa a kowanna matakai na Kasar Nan duba da sune masu jini a jika Kuma lokaci da su yake damawa a kan kadamin su.
Kazalika yayi Kira ga matasa su bashi gudun mawa Alan wannan takara tashi.
Acewar sa tuni ya gana da shugaba Buhari da Mai dakin shugaban Kuma sun bashi kwarin guiwar tsayawa takarar.