Har yanzu dai tsugunne bata kare ba game da rikicin da ya barke tsakanin jarumi Ali Nuhu da jaruma Hannatu Bashir, wacce har ta kai su ga zuwa gaban kotu.
Wata kotun majistiri mai lamba 58, karkashin mai shari’a Aminu Gabari, ta bayar da umurnin cewa dole jaruma kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Hannatu Bashir ta gurfana a gabanta.
Lauyoyi sun bukaci da a basu dama su yi sasanci
Kotun dai ta fara sauraron karar da babban jarumin masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, ya shigar akan jaruma Hannatu Bashir dangane da zargin da yake mata na cin zarafinsa.
Yayin zaman kotun wanda ya gudana a ranar Talata, lauyoyin mai kara da lauyoyin wacce ake kara sun bayyana a gaban kotun, inda suka bukaci kotun da ta amince musu su je suyi sasanci.
Sai dai kotun taki amincewa da wannan bukatar ta su inda ta bayar da umurnin dole waccea aka yi kara, wato Hannatu Bashir ta bayyana a gaban Kotu.
Kotun ta sanya ranar 25 ga wannan watan Oktoban da muke ciki, domin ci gaba da gudanar da shari’ar.