Amaryar fitaccen mawaki sannan jarumi Shuaibu Ahmed Idris wanda aka fi sani da Lilin Baba, wacce ita ma tsohuwar jarumar Kannywood ce, Ummi Rahab, ta sanar da cewa tana dauke da juna biyu.
Amaryar ta bayar da wannan sanarwan ne a shafinta na Instagram inda ta saka hoton ta sanye da atamfa ja tana zaune a kujera cike da murmushi.
Tsohuwar jarumar ta bukaci masoyanta da su taya ta da murna inda tayi alkawarin tukuicin katin waya ga mutum 50 na farko da suka fara saka sakon taya murna a kasan hotonta.
A cewarta: “In har na samu tsokaci ta hanyar rubuta ‘Congratulations’ a karkashin wannan hoton, zan bada kyautar kati ga mutane 50.”
Sai dai kuma jarumar bata sanar da katin nawa zata bai wa kowanne mutum ba da yayi tsokaci.