Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta tarayya wato Standard Orgaizastion of Nigeria Son, a turance ta bude sabon ofishin ta da zai rinka lura da shiyyar arewa maso gabashin kasar nan a jihar Bauchi da zummar tabbatar da ganin an samar da kayayyaki masu inganci da nagarta a kasar nan.
Yayin bikin bude ofishin, shugaban hukumar ya ce, gwamnati ta damu mutuka bisa karuwar kayayyaki marasa inganci a manyan kasuwannin kasar nan
Babban ofishin wanda ’yan kasuwa da masana`antun dake jihohin Gombe da Taraba da Borno da Yobe da kuma Adamawa za su rinka amfani da shi wajen tantance ingancin kayayyakin da suke sarrafawa ko kuma sayarwa.
Bikin wanda ya samu halartar karamar minista a ma`aikatar masana`antu da harkokin zuba jari ta kasa Ambasador Maryam Katagun.
Tun da fari babban shugaban hukumar SON, Mal Faruk A Salim ya ce babu kasar da za ta ci gaba ta fuskar harkokin kasuwanci da cinikayya a daidai lokacin da masana`antun kasar suka gaza samar da kayayyaki masu inganci wadanda kuma za su karbu a ko’ina a duniya.
Ya ce ’yan Najeriya da sauran baki dake zuwa kasuwanci daga kasashe makwafta sun sha gabatar da korafin su ga hukumar game da kayan jabu.
Salim ya ce “Mun kaddamar da babban ofishin mu ne na shiyya da kuma na jihar Bauchi, inda a cikin wannan ofishi akwai magwaji wato na’urar fasahar Aune-Aunen kaya wanda suka kama da kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum, wanda a yanzu haka shi ne irinsa na farko a arewacin Najeriya baya ga wanda muke da shi a jihar Legas. Yanzu ’yan kasuwa daga arewacin Najeriya za su rinka kawo samfurin kayayyakinsu domin a gwada ingancinsu, wannan zai taimaka sosai wajen inganta harkokin kasuwanci da bunkasuwar masana’antu a shiyyar baki daya.”
A nata bangaren, karamar minista a ma’aikatar masana’antu da harkokin zuba jari ta tarayyar Najeriya Ambasada Maryam Katagum ta bayyana samar da wannan ofis a matsayin wata babbar nasara da gwamnatin shugaba Buhari ta samu wajen ingantawa da bunkasa harkokin kasuwanci a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Ministar ta kuma ja hankalin ’yan kasuwa da masu masana`antu a shiyyar da su himmatu wajen bin doka da oda ta hanyar samar da kayayyaki masu nagarta.
“Samar da ofishin shiyyar zai bude kofar cinikayya ba wai kawai aikin tantance ingancin kayayyaki ba, samar da dakin gwaje-gwaje da aka yi tamkar wani sinadari ne da zai tabbatar da bunkasuwar kasuwanci gaba daya.”
Kazalika karamar ministar ma’aikatar kasuwanci da harkokin zuba jari ta tarayyar Najeriya ta sanar da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya za ta mayar da hankali sosai wajen ganin an farfado da masana’antar sarrafa nama dake garin Bauchi domin ya kasance yana fitar da nama zuwa kasashen duniya domin habaka tattalin arzikin kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)