Najeriya na shirin sayo jiragen yaki da wasu makamai na Dala biliyan guda

Kasar Amurka ta dawo da yarjejeniyar sayar da jiragen yaki masu saukar Angulu da sauran makaman yaki ga gwamnatin Najeriya wanda ta dakatar a baya biyo bayan abin ta kira take hakkin dan Adam da Najeriya take yi a baya.

 

Maaikatar tsaro ta kasar Amurka itace ta sanar da dawo da yarjejeniyar siyarwa da Najeriya jiragen yaki masu kirar 12AH -1Z akan kudi kimanin Dalar Amurka biliyan guda.

 

Da ake yantawa da shi Bob Menendez yace akwai Bukatar gwamnatin Najeriya ta mayar da hankalin ta wajan yakar matsalolin tsaro da yake addabar sassan kasar.

 

Tuni shugaban kasa Muhammad Buhari ya gana da shugabannin tsaro akan lamarin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments