Amfanin shan ruwan Dumi kullum da safe

kwararrun Likitoci suna bada shawarar cewa  mutane da su yawaita shan ruwan dumi musamman da safe domin samun karin lafiya ajikinsu.

Masana harkar Lafiya  sun gudanar da bincike akan amfanin da shan ruwan dumi ke yi a jikin mutum musamman idan ana sha ruwan da safe kafin a karya.

Binciken ya nuna cewa shan ruwan dumi na bunkasa  lafiyar mutum sannan yana hana tsufa da sauri.

Likitocin sun bayana wasu amfani da shan ruwan dumi ke yi a jikin mutum kamar haka;

1. Shan ruwan dumi na hana tsufa da sauri.

2. Yana taimakawa wajen nika abinci da sauri.

3. Yana kawar da laulayin al’ada na wata wata da wasu matan ke yi.

4. Yana taimaka wa mutum wajen yin bayan gida musamman a kananan yara.

5. Yana kawar da kaikayin makogworo.

6. Yana taimaka wajen rage kiba

7. Shan ruwan dumi na rage murdewan ciki.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments