Mai martaba sarkin kano na 15 a jerin sarakunan fulani Alhaji aminu ado bayero ya samu kansa a wannan duniya a ranar 21-8-1961 inda a daidai wannan rana yake cika shekara 61
Daga wakilin aksammedia B.imam
Mai martaba sarkin kano kamin ya hau kan kujerar mulkin gidan dabo ya rike mukamai na sarauta daban daban kamar yadda aka sani duk dan sarki indai ya cancanci a nada shi sarauta ana nada shi mai martaba saida ya rike mukamin wanban kano sannan Allah ya daga likkafar sa zuwa sarkin bichi na farko a tarihi bayan ya idda shekarun da Allah yasa zaiyi a bichi ne sai mai girma gwamnan jihar kano ya nada shi a matsayin sarkin kano na 15 a jerin sarakunan fulani
Mai magana da yawun masarautar kano abubakar balarabe kofar na’isa ya shiga sahun masu taya mai martaba murnar cika wadannan shekaru