A wani faifen video dake yawa a kafafen sada zumunta anga yadda yan taadda masu garkuwa da mutane suke yiwa wadanda suka kama bugun dawa da sanduna.
Bayan shegen duka da aka yiwa mutanen da aka yi garkuwa da su daga bisani sun tayar da mutun daya daga cikin su akan yayi jawabin halin da suke ciki inda ya roki kasashen turawan yamma da su shiga maganar ceto su daga halin da suke.
A jawabin nasa yace rashin haline ya saka suke rike hannun yan taaddar har kawo yanzu.
Daga bisani ana rokon yan uwa su saka su a cikin addua Allah ya kubutar dasu daga cikin ahalin da suke ciki