Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’umar jihar Kano su zama masu bin dokokin Kasa.
Sarkin na Kano ya bukaci hakan ne lokacin da Sabon Kwanturola na hukumar Custom mai kula da jihohin kano da jigawa yakai masa ziyara a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Jami’an Hukumar ta kwastam su zama masu fadakar da al’umma dokoki tareda kiyayesu.
Kazalika Sarkin na kano yayi musu Nasiha akan su zama masu tausayawa al’uma tareda gyara musu kurakuransu ta hanyar masalaha idan har akwaita wadda bazata sabawa doka ba.
Tun da farko sabon Kwanturolan Kwastam din mai kula da Kano da Jigawa, Mu’azu Hassan Raji, ya ce jihar Kano nada matsayi mai muhimmancin gaske a hukumar kwastam ta ƙasa, ya ƙara da cewa hukumar na samun zunzurutun kuɗaɗen shiga har Naira biliyan hudu a a kowanne wata a jihar Kano
Ya kuma shaida wa Sarkin Kano cewa, sun zo fadar sa ne domin ya gabatar da kansa da neman tubarraki da kuma goyon baya da hadin kai domin ya samu nasarar aiwatar da aikin da aka turo shi yayi, tare da jaddada kudurin hukumar na inganta ayyukansu a yankin Kano da Jigawa da ƙasa baki ɗaya.
A wani labarin kuma Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya amince da nadin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin babban Limamin masallacin Jami’ar Skyline da ke birnin Kano.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Press Secretary to Kano Emirate Council
15th SEPTEMBER, 2022