‘Abin da ya kamata Najeriya ta yi don magance raɗaɗin hauhawar farashin kaya’
Daga Walid Y Hari.
Masana tattalin arziki a Najeriya na fargabar cewa za a iya samun karuwar wadanda ke fadawa cikin kangin talauci matukar aka ci gaba da samun hauhawar farashin kayan masarufi, kamar yadda yake faruwa a ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumar kididdigar kasar ta ce an samu karin hauhawan farashin kayan abinci da fiye da kashi ashirin cikin dari a cikin watan Agustan da ya gabata.
Hukumar ta ce wannan ne hauhawar farashi mafi girma da aka samu a Najeriya a cikin shekaru goma sha bakwai da suka wuce.
Masana irinsu Dakta Shamsuddeen Muhammad na Jami’ar Bayero ta Kano sun bayyana cewa wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnati ta bijiro da su na taka rawa wajen ƙara hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
Shamsuddeen.
Bayanan hukumar ƙididdigar ta Najeriya dai na nuna cewa jihar Kwara ce kan gaba da fiye da kashi 30 cikin 100, sai jihar Ebonyi da Rivers da ke bi ye mata yayin da Jigawa da Zamfara da Oyo suke tafe.