Man Fetur: NMDPRA ta gaza fadawa yan kasa farashin gwamnati

Rahotanni na nuni da cewa gwamnatin tarayya na sane da  karin farashin man fetur daga   Naira 165 zuwz 185 a sassan kasa nan, kuma gwamnati ce ta bada umarnin daukar  matakin hakan kamar yadda masu hada-hadar man suka shedawa manema labarai.

Radio Faransa ta ruwaito cewa Kawo yanzu Hukumar da ke Kula da Albarkatun Mai na Ruwa da kan Tudu ta kasa NMDPRA ta gaza cewa  uffan game da matakin kara farashin man da kawo yanzu ake neman shafe wata guda.

Kazalika tace Wasu bayanai sun nuna cewa, karin farashin ya fara aiki daga yau Talata, inda har aka sayar da lita guda akan Naira 179 daga 165 a yankin kudu maso yammaci da kudu maso kudanci da kuma kudu maso gabashin kasar.

A arewa maso yammacin Najeriya kuwa, farashin ya kai Naira 184 , sannan ana sayar da lita guda akan Naira 189 a yankin arewa maso gabashin kasar, abin da ke nufin an kara Naira 24 kai tsaye

Za a ci gaba da sayar da man fetur din akan Naira 179 a yankin tsakiyar arewacin kasar, yayin da a birnin Lagos za a ci gaba da sayar da farashin akan Naira 169, sannan kuma a Abuja farashin zai kasance akan Naira 174.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments