Yadda al’ummomin karamar hukumar Wase da Kanam suke fuskantar matsin lamba daga yan bindiga

Al’ummomin wasu yankunan na kananan hukumomin Wase da Kanam dake Jihar Filato sun koka bisa yadda ‘yan taadda  ke yiwa mutane kisan gilla kuma suke sace dabbobi tare da yin garkuwa da wasu mutanen a kauyukansu.

A wannan lokaci  lamarin tsaro ya tsananta a kauyukan dake kan iyakokin jihohin Filato, Taraba da Bauchi, inda ‘yan bindiga suka tsaurara kai hare-hare suke kuma sace mutane, Da dabbobi tare da kisan wasu mutanen.

Inusa Jarmai Shugaba ne na kasuwar shanu a garin Jarmai dake karamar hukumar Wase, yace ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu fiye da dari biyar bayan sace mutane da har yanzu baa san adadin su ba a ranar Jumma’ar da ta gabata.

Shima kansila mai wakiltar Gimbi da Pinau a karamar hukumar Wase, Adam Umar yace ‘yan bindiga sun kori manoma da makiyaya dake rayuwa a kauyukan yankin da dama.

Kakakin rundunar dake samar da zaman lafiya a Jahar Filato, Manjo Ishaku Takwa a sakon kar-ta-kwana ya shaida wa muryar Amurka cewa ‘’Wase na can, hankali kwance’’.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments