Shugaban Gidauniyar Tallafawa Marayu Da Mabukata Da Samar Da Ruwan-Sha Da Wayar Dakan Alumma Illolin Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Da Inganta Tarbiyar Addinin Musulunci wanda Ke Da Cibiya a Kaar Masar, Wanda kuma Shine Shugaban Kungiyar Tsafaffin Daliban Babbar Makarantar Ilmin Addinin Musulunci Dake Al’azzahar a wanñan Kasa Dr Ahammad Muhammad Abubakar Tunga ya Jaddda Kuddirin Kungiyar na Tallafawa Marayu Da Mabukata Da Samar da Ruwan-Sha Da Ilmantar Da Alumma Hanyoyin Koyawa ‘Yay’yansu Tarbiya Dan Kaucewa ‘Dabiar Nan Ta Shan Miyagun Kwayoyi Dan Samun Alumma Tagari
Daga Dantala Uba Nuhu Kura
Ya jaddada Hakan Ne Yayin Da Kungiyar Ta Jagoranci Babban Taronta Data Sabayi a fadin Kasar Nan Wanda Ta Gudanar a Babban Masallacinn Nana Aisha a Karamar Hukumar Kura Maitaken Tarbiya a Musulunci Da Illolin Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi a Cikin Alumma.
Tunda Fari Iman Dr Samaila Ali Kura Daga Jamiar Madinah Ya Bayyana Illolin Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Da Yadda Suke ‘Bata Kwkwalwa Ga Rayuwar Alumma a Addinin Musulunci Inda Ya Hori Iyaye Da Mahukunta Da Malamai Dama Sauran Alumma Dasu Kara Kaimu Wajan Sanya Ido Da Hana Wanñan Muggar Dabia Da Take Nema Ta Zama Ruwan Dare a Cikin Alumma
Dr Samaila Kura Ya Bayyana Yawaitar Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Mussmmssn Ga Mata Da Matasa a matsayin hanyar gurbacewar tarbiya Daga Nan Yayi Adduar Fatan Shiriya Da Yiwa Kasa Adduoin Cigaba Da Samun Zaman Lafiya Da Karuwar Arziki
Shima Da Yake Taaliki Kan Bayanan Da Malamai Suka Gudanar
Sheik Imam Dr Abdulazziz Ibrahim Bsuci
Yayi Taaliki Mai-Tsawo Kan Illolin Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Da Gurbacewar Tarbiya Ga Mata Da Matasa a Cikin Alumma.
Dr Abdulazziz Ibrahim Bsuci Ya Kuma Bayyana Hanyoyin Samun Sassauci Da Magance Matsalolin a Addinin Musulunci Ya Kuma Bayyana Muhinmancin Tarbiya Ga Alumma
Cikin Wadanda Sukayi Jawabi Sun Hada Da Sheik Alkali Abubakar Sumaila Wanda Yaja Hankalin Iyaye Wajan Kulawa Da Tarbiyar Yayansu Dan Samun Alumma Tagari
Daga Karshe Taron Ya Sami Wskilcin Dokajin Rano Hakimin Kura Abubakar Tijjani Abubakar Da Sarkin Kanwa Alh Isyaku Maitama Kura Da Galadiman Garun-Malam Da Sarkin Makeran Kura Da Shugabannin Kungiyar Tsofaffin Daliban Na Kura Sheik Abdulrauf Nasidi Da Khalid Abubakar Da Aluma Da Dama.