Champions League: Abin da ya kamata ku sani kan wasannin Talata.
Daga Walid Y Hari.
Za a ci gaba da wasanni na biyu a cikin rukuni a Champions League, inda za a kara a fafatawa bakwai ranar Talata.
Rukuni na daya da na biyu da na uku da kuma na hudu ne za su buga wasa na bibiyu.
Liverpool da Ajax Amsterdam
Liverpool da Ajax sun kara sau hudu a Gasar Zakarun Turai, inda Liverpool ta ci wasa biyu, Ajax ta yi nasara daya da canjaras daya.
Rukuni na biyu.
A rukuni na biyun za a fafata tsakanin Bayer 04 Leverkusen da Atletico Madrid.
Haka kuma a rukunin na uku FC Porto za ta karbi bakuncin Club Brugge.
Rukuni na uku.
Za a fafata tsakanin FC Bayern Munich da Barcelona a wani wasa mafi zafi.
Daya wasan na rukuni na ukun za a yi ne tsakanin FC Viktoria Plzen da Inter Milan.
Rukuni na hudu.
Za a kai ruwa rana tsakanin Sporting da Tottenham.
Daya wasan shi ne tsakanin Olympique Marseille da Eintracht Frankfurt.