Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace katin Dan kasa yana da muhimmanci a wajen al’ummar kasar nan duba da yanda al’umma suke yawan tafiye tafiye zuwa kasashen waje.
Mai martaba sarkin ya bayyana haka ne lokacin da Shugaban Hukumar Kula da Katin Dan Kasa wato National Identity Management Agency (NIMA) suka kawo masa ziyara a fadarsa.
Mai Martaba Sarkin wanda Madakin Kano ya wakilta yace Masarautar kano zata mara musu baya wajen fadakar da dagatai da masu unguwanni don sanin mahimmanci katin Dan kasa.
A nasa jawabin shugaban Hukumar Kula da Katin Dan Kasa, wato National Identity Management Agency Alhaji Abdullahi Ahmed yace sunzo fadar Masarautar Kano ne don neman goyon bayan masarauta don samun nasarar gudanar da aiyukansu don jama’a su fahimcin muhinmancin Katin Dan kasa.
Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya rawaito cewa masarautar ta kano zata basu hadin kai da goyon baya wajen fadakar da al’umma kan mahimmaci katin Dan kasa yake dashi.
A lokacin ziyarar dai Shugaban Hukumar kula da katin shaidar Dan kasa Alhaji Abdullahi Ahmed yana tareda Daraktoci da sauran manyan ma’aikatan Hukumar.
Daga magatakardar yada labarai na masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa