Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, yakai ziyarar ta’aziyyar Sarauniyar England Queen Elizabeth ll.
The Emir Of Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci ofishin Jakadancin Kasar England dake Abuja domin yin ta’aziyar mutuwar Queen Elizabeth ll wadda ta mutu a makon da ya gabata.
Press Secretary na Sarkin Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa yace Sarkin Kano Aminu Bayero ya nuna alhininsa bisa rasuwar Queen Elizabeth wanda ya bayyana ta da cewar rashi ne na duniya baki daya tareda bayyana wasu kyawawan halaeyenta.
Da yake sanya hannu a littafin ziyarar ta’aziyyar Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi fatan wanda ya gajeta zai dora daga irin cigaban data kawo a bangarori daban daban.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Chief Press Secretary to Kano Emirate Council
12/9/2022