Atletico Madrid za ta saurari kungiyoyin da ke son sayen Joao Felix, dan wasan gaban kungiyar mai shekara 22, wanda Manchester United ta so saya a karshen kakar bara. (Cedena SER via Express)
Tottenham ta cimma yarjejeniya da Atalanta domin sayen dan wasanta na tsakiya Ruslan Malinovskyi mai shekara 29 a watan Janairu mai zuwa. (Il Giorno via Express)
Leicester City kuwa na sa idonta kan dan wasan tsakiya na kungiyat Lorient ta Faransa Enzo le Fee mai shekara 22 domin ya maye gurbin Youri Tielemans dan kasar Belgium mai shekara 25. (90min)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce zai kalli dukkan abubuwan da ke gabansa kafin ya yanke hukunci kan irin ‘yan wasan da kungiyar ke nema domin a karfafa ta domin ta iya lashe gasa firimiyar Ingila a bana. (Express)
Arteta na son sayo wasu ‘yan wasan da za su inganta kungiyar ta Arsenal, inda ya fi mayar da hankali kan sayo Facundo Torres dan wasan gefe na kungiyar Orlando City mai shekara 22, da kuma Mykhaylo Mudryk shi ma dan wasan gefe mai shekara 21. (Mail)
Aston Villa ta sa Pau Torres, dan wasan baya na Sfaniya mai shekara 25 cikin ‘yan wasa da a ke sha’awar sayowa tun bayan da ta dauki sabon koci Unai Emery, wanda ya taba horas da shi a kungiyar Villareal. (Football Insider)
West Ham United ta shiga sahun kungiyoyi kamar Southamton da Leicester City da kung Brentford domin sayen Tete, dan wasan gefe dan kasar Brazil mai shekara 22, wanda a halin yanzu yana matsayin dan aro ne a Shakhtar Donetsk. (Sun)
Sabon kwantiragin Lionel Messi a Paris St Germain ta hada da wani sharadi da zai ba dan kasar Ajentinan mai shekara 35 ya fi mayar da hankalinsa kan taimaka wa kasarsa yayin da ake hasashen wannan ne gasar cin kofin duniya na karshe da zai halarta. (TN via Express)
Liverpool na shirin tattaunawa da dan wasanta na gaba, Roberto Firmino mai shekara 31 kuma dan kasar Brazil, da zummar tsawaita zamansa a Anfield. (Football Insider)
Wolverhampton Wanderers na fatan nada Julen Lopetegui a matsayin sabon kocinta a ranar 13 ga watan nan na Nuwamba, ranar da za ta kara da Arsenal kafin a tafi hutu a gasar firimiyar Ingila saboda gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar. (Mail)