An bayyana koma baya da aka samu a Fannin kayayyakin amfanin gona a wannan shekarar sakamakon ambaliyar Ruwa da manoma suka samu a wasu daga cikin jihohin arewacin kasar nan a matsayin rashin daukar mataki a lokacin da ya dace.
Zababben Sakataren kungiyar kasuwar abinci ta Duniya dake Dawanau karamar hukumar Dawakin Tofa kwamaret Rabiu Abubakar Tumfafi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da yadda wannan shekarar ta zo da Shi a bangaren kayayyakin amfanin gona, Wanda ya gudana anan Kano.
Rabiu Tumfafi, yace kasancewar an samu ambaliyar Ruwa, ya Sanya manomada yankasuwar kayayyakin abinci sun samu tasgaro da koma baya a kasuwancinsu Wanda kayan amfanin gona sun yi karanci, musamman masu fita da Shi zuwa kasashen waje domin yiñ kasuwancinsu.
Sakataren kungiyar kasuwar ta Dawanau, yace kasancewar kasuwar abinci ta Dawanau kasuwace ta Duniya, ya Sanya shugabancin kasuwar yake da managartan tsare_tsare domin ganin ya tallafawa kananan yankasuwar yadda za su koyi fitar da kayayyakin amfanin gona da ake samarwa a nan cikin gida Najeriya, Wanda yin haka zai Kara bunkasa tattalin arzikin jihar Kano da ma kasa Baki daya.
Ya bukaci Gwamnatin tarayya dana jihohin arewacin kasar nan, da su bijiro da wasu hanyoyi da zasu tallafawa manoma da yankasuwa bisa yawan asara da suke samu da tasgaro a lokuta daban daban, musamman lokacin damuna wajen yawaitar Ambaliyar Ruwa.
Tumfafi yace, akwai bukatar Gwamnatin tarayya ta baiwa fannin harkokin kayayyakin amfanin gona mahimmanci, maimakon dogaro da fannin man fetur, domin yin gogayya da sauran kasashen waje.
Yace rashin baiwa fannin harkokin kayayyakin amfanin gona mahimmanci, Yana haifar da tsadar kayayyakin abinci a cikin gida Najeriya, Wanda Bai kamata hakan ta kasance saboda Allah ya albarkaci Najeriya da kasar Noma fiye da sauran kasashen waje.
Inda yace, Najeriya tana noma shinkafa da wake da gyada da waken suya da masara da Dawa da gero da dai sauran kayayyakin amfanin gona, Wanda wannan ba karamin abin alfahari bane ga alummar kasar nan ba.
Haka zalika yace, yankasuwar da suke safarar kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen ketare ba karamin kalubale suke fuskanta ba, yakamata Gwamnatoci a matakai daban daban su kawo musu daukin gaggawa domin ganin an bunkasa fannin harkokin kayayyakin amfanin gona.
Wannan na daga cikin dalilan daya Sanya shugabancin kungiyar kasuwar abinci ta Duniya dake Dawanau ta jajirce wajen wayar da Kan yankasuwar amfanin dake cikin safarar kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen ketare maimakon dogaro da Wanda za, a shigo da su gida Najeriya, Wanda Kuma, idon aka inganta su ya fi Wanda za, a shigo Mana da Shi.
Daga karshe ya yayi Kira ga alummar kasuwar abinci ta Duniya dake Dawanau, da su ci gaba da baiwa shugabancin kasuwar cikakken hadin Kai da goyan bayan daya dace, domin samun damar bijiro da managartan shirye shirye da za su bunkasa kasuwancinsu da farfado da tattalin arzikin jihar Kano da ma kasa Baki daya.
(Ibrahim sani gama pyramid radio. )