An yi Kira ga mawadata da masu hannu da shuni da su tallafawa marayu da masu karamin karfi da kuma masu bukata ta musamman duba da karatowar sallar layya domin jin dadin bukukuwan sallah kamar kowa.
Sakataren kungiyar kasuwar abinci ta duniya dake Dawanau a karamar hukumar dawakin tofa Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi ne yayi wannan kiran a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Rabiu tumfafi yace marayu da dama da masu karamin karfi na bukatar tallafi musamman yadda yanzu al,amura suka cakude kayayyakin masarufi sun yi tsada man fetur da gas da sauran abubuwan amfanin yau da kullun.,a don haka yake kira ga alumma suyi amfani da damar da Allah ya basu wajen taimakawa talakawa da marayu da kuma masu bukata ta musamman.
Tumfafi Ya kuma yi Kira ga Gwamnatin jihar Kano da Manyan yan kasuwa dasu hada kai da kungiyar kasuwar abinci ta duniya domin bijiro da managartan tsare tsare yadda kasuwar zata kara habaka da samarwa gwamnati kudaden haraji fiye da yadda take samu a halin yanzu.
Yace kuginyar kasuwar kofarta a bude take wajen shigewa yan kasuwar gaba domin hada hannu da majalisar kula da harkokin fitar da kayayyaki kasashen waje ta kasa domin ciyar da jihar Kano gaba da ma kasa baki daya.
Haka zalika Sakataren kungiyar kasuwar yace yin hakan zai karawa kasarnan karfin tattalin arziki ta fannonin kasuwanci duba da kasashe da dama suna shigowa domin siyayya. amma da dama wasu yan kasuwar basu gane amfanin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare ba.
Kwamared Tumfafi Ya kara da cewar sun gayyato Bankuna da dama cikin kasuwar don baiwa yan kasuwa rancen jari ta yadda daga baya za su rika biya da kadan kadan, inda yace a yanzu haka sun karbi samfurin fama famai Wanda suka rarraba ga yan kasuwar don bunkasar tattalin arzikin kasuwar.