Rashin riko da sanaar hanu ke jefa matasa cikin kaka nakayi: Zannira isa ibrahim

Matashiyar dai tayi kira ga matasa musamman mata masu tashi su nemi na kansu domin hucewa kansu takaici.

Daga wakilin aksammedia B.imam

Tayi kiran ne a yayin wata hira data gabatar ta cikin shirin guntun gatarin ka dake zuwa daga gidan radio kano uwa mabada mama.

Zannira dai matashiya ce wacce aka haife ta a unguwar mandawari dake karamar hukumar gwalen birnin jihar kano an haifi matashiyar a shekara ta 2000 tayi karatuttukan ta na islamiyya a wannan unguwa tasu sannan tayi karatun zamani kar zuwa yanzu da take kwalejin gwamnatin tarayya ta kano wato FCE.

Zannira dai ta rungumi sana’ar kera takalma na maza da mata amma tafi karfi ana maza yadda idan ta kera maka takalmi kai kace daga kasar italiya akai jigilar sa ta kasance tana gudanar da wannan sana’a a kasuwar kofar wambai dake birnin jihar kano.

Ta bayyana cewa ta samu horan ilimin hada takalma sanadiyyar wata kungiya data ke daukan marasa karfi da marayu wani lokacin ma hadda masu karfin.

Domin neman karin bayani kwa iya tintibar ta a lambar waya kamar haka 08060309646

 

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments