Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC daga ofishinta dake Osogbo na jihar Osun ta bayyan Adeleke, a matsayin wanda ya samu nasara da kuri’u 403,371 a zaben na ranar Asabar, tare da ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Zababben gwamnan dai ya sha kaye a zaben 2018 a hannun Gwamna Adegboyega Oyetola amma bayan shekaru hudu ya samu nasarar tsige abokin takararsa wanda ya samu kuri’u 375, 027.
Koma baya ga APC
Manazarta na cewa, hakan babar koma baya ce ga Jam’iyyar APC mai Mulki na rasa daya daga cikin jahohin da take rike da madafun iko, al’amarin da ka iya zamewa jam’iyyar adawa ta PDP gaba a zaben 2023 mai zuwa.
Duk da cewa jam’iyyun siyasa 15 ne suka halarci atisayen, amma gasar dawaki biyu ce tsakanin PDP da APC.
Manuniyar zaben 2023
Zaben Osun kasancewar shi ne zabe na karshe kafin zaben 2023, wata hanya ce da manyan jam’iyyu za su gwada karfin su kafin shekara mai zuwa.