Kalaman Jagoran kwankwasiya na kasa Akan matasa

Wasu daga cikin Muhimman batutuwa na siyasa da Jagora kwankwaso yai magana akai a hiransa ta yau 19-2-2022

1-Sai kaga mutum saboda yana ma’amula da ƴan bori sai a ɗora shi a keken Ɓera, wai shi dole sai yayi Gwamna.

2-Mutum sai yaje ya ɗauki kansa yasa a sikeli, nauyinsa baifi kilo biyu ba amma yace nauyinsa kilo ɗari ne.

3-Burinmu shine mu dasa taurari a kowanne gida a faɗin Nigeria ya zamanto sun zamo masu daraja abun alfahari

4-In kace mutum yazo yayi State Assembly sai yace shi yafi ƙarfin yayi assembly saboda ya taɓa yin Kwamishina, ko yayi wani muƙami.

5-Koh ni Rabiu Kwankwaso ban fi ƙarfin na koma Kwankwaso nayi Kansila ba.

6-Ba’a shuka ƙarangiya a girbi alkama 👌

7-Da APC da PDP dukkanin su basu da abin da zasu tallata kansu a wajen ƴan ƙasa

8-Shi mai hassada ba sai kayi masa laifi ba, laifin kawai shine mun fisu Daraja.

9-Burin mu duk yaran nan da muka biyawa kuɗin makaranta su taso su fimu komai na cigaban rayuwa.

10-A tsari na Kwankwasiyya ba wanda muke so ya tafi amma duk wanda yace zai tafi ya barmu zamu ce da shi a sauka lafiya.

11-Muna buƙatar kowa da kowa a tafiyar Kwankwasiyya amma son samu ne mun fi buƙatar mutanen da bamu taɓa mu’amalar siyasa da su ba domin su zo suga yadda muke tafiyar mu.

12-Duk wanda suke cewa zasu bar tsarin kwankwasiyya suje a ci daɗi lafiya, amma dai idan mutum ƙaninka ne hakan ba zata saka yace ya zaman yayan ka ba.

13-Matasa “Yanzu sune shugabanni, sune karfin tafiyar nan”

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments