Nazarin da wani lauya Mai fafutukar Kare hakin Dan Adam yayi Mai suna, Bulama Bukarti, yace,
Daga 1999 zuwa yau, ASUU ta yi yajin aiki sau 16 na jimillar tsawon watanni 51. A kowanne shekaru biyar, ASUU tana yajin kimanin shekara daya. Kenan a kowanne shekara biyar laccara yana kar6ar albashin shekara daya ba tare da yayi aiki ba. Sannan kusan duk wanda ya gama jami’ar gwamnati a Najeriya, to yayi asarar kusan shekara guda saboda yajin aiki. ‘Yan siyasarmu ba su damu ba saboda basa tausayinmu. Su kuma ‘yan ASUU sun gaza fito da hanyar za ta 6ulle, kuma ba za to cutar da dalibai ba.
Yanzu idan aka gama wata dayan nan, ASUU za su shiga yanin aikin sai-baba-ta-gani. Suma ‘yan siyasa suna can suna harkokin siyasar 2023. Fisabillah, ta yaya mai tunani zai goyi bayan wannan? Ta yaya wannan zai zama aiki da hankali? Yanzu Buhari zai gagara barci saboda ana yajin aiki. Banda ministocin ilimi da dama wadanda ‘yan’yan ASUU ne, hatta shugabanni kasa biyu tsoffi ‘yan ‘yan ASUU sun gaza magance matsalar nan.
Amma abin mamaki, sai ka ga wadanda da kamar za su mutu don haushi idan aka yi yajin aiki, yanzu suna goyon bayan yajin aiki saboda jifa ya wuce kansu. Lokacin da ina dalibi ban goyi bayan yajin aiki ba. Lokacin da na koyar ban goyin bayan yajin aiki ba. Kuma yanzu ma bana goyon ba. Kuma wallahi da ASUU za ta bawa kowa za6i, malamai da dama za su je su koyar da dalibansu, Dalili kuwa shine: wannan salo bai magance matsalar ba kuma yana cutar da dalibai.
Mu cire son rai da kiyayya ko soyayya, mu ji tsoron Allah, mu duba gaskiya. Daga kin gaskiya, sai bazama daji. Ita kuma gaskiya nan bata buqatar ado.