Shaidun gani da ido sun ce jirgin na cin wuta kuma sun ji karar fashewar abubuwa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Athens ya ruwaito.
Jami’an yankin sun ce an tura motocin kashe gobara bakwai zuwa wurin da hatsarin ya faru amma ba za su iya isa ba saboda fashe-fashen da ke ci gaba da aukuwa a jirgin.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce jirgin dakon kaya ya taso ne daga Sabiya zuwa kasar Jordan, kuma ya bukaci a ba shi izinin yin saukar gaggawa a filin jirgin saman Kavala da ke kusa, amma bai samu isa tashar ba.
Tashar talabijin ta ERT ta gwamnati ta bayar da rahoton cewa, jirgin na kasar Ukraine ne, wanda a cewar mutanen kauyen tuni ya fara cin wuta kafin ya fado.
Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumance game da adadin mutanen da ke cikin jirgin da ke ci gaba da konewa kamar yadda faifan bidiyo da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na kasar suka nuna.
Sai dai ERT ta ruwaito cewa jirgin na dauke da mutane 8 kuma kayan da yake da su na da hadari. Rahoton ya kara da cewa ‘yan sanda sun bukaci ‘yan jarida da ke wurin da su sanya abin rufe fuska.