Dan takarar gwamnan jihar katsina na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, a zaben da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Dan Marke, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe ta bayyana.
Cikin wata hira da ya yi da manema labarai, Sanata Lado, ya ce, zabe ne mai cike da magudi, da aringizon kuri’u, da barazana ga masu zabe, da dai duk wani ha’incin da bai taba gani a harkar zabe ba.
Ya ce,” Ba mu gamsu da wannan sakamakon zabe ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zaba bane aka bayyana.”
Dan takarar gwamna na jam’iyyar ta PDP, ya ce, yakamata a daina yin zabe kawai a rinka yin nadi, don yana ga hakan ya fi alkhairi.