Rahotanni na nuni da cewa jam’iyun adawa da suka yi takarar gwamnan a jihar Kaduna sun yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar wanda ta ayyana Dan takarar jam’iyar APC sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar
Jam’iyun da suka yi watsi da sakamakon zaben sun hadar da babbar jam’iyar adawa ta PDP da, Isah Ashiru Kudan, yayi wa takara sai jam’iyar NNPP da, Sen. Suleiman Hunkuyi, yayi wa takara