Jam’iyar APGA tazo da sabon salo na rantsar da gwamna da mutane 50

Rahotanni na nuni da cewa Wasu daga cikin mazauna garin Akwa, babban birnin jihar Anambra sun yi tir da yadda aka hana su halartar bikin rantsar da sabon gwamna.
Tun da fari dai Babban Darektan kwamitin yakin neman zaben Farfesa Soludo a zaben 2021, C-Don Adinuba, ya bada sanarwar cewa mutane 50 kadau aka gayyata zuwa bikin rantsar da sabon gwamnan.
Mataki da aka dauka bai yi wa al’umma dadi ba.
 Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN yaji ta bakin mutane a gari, da-dama sun nuna ba su taba ganin irin haka ba.
  Wani mazaunin gari Mai suna, Chidiebere Igbokwe ya ce rantsar da gwamna babban biki ne da yake jawo jama’a daga ko ina, don haka ba daidai ba ne a hana su zuwa.
Chidiebere Igbokwe ya ce wannan ce al’ada tun daga zamanin mulkin soja har zuwa yau a jihar.
Kazalika wani lauya Mai suna Sunny Orji mazauni Awka, ya ce ba daidai ba ne Farfesa Soludo ya hana wadanda suka zabe shi zuwa wajen bikin rantsar da shi a matsayin gwamna.

Jagororin jam’iyyar APGA irinsu Shedrack Nwosu sun nuna ba su san abin da ake ciki ba. Rahoton ya ce duka-duka, ‘yan jarida hudu aka gayyata bikin. Charles Chukwuma Soludo ya ci zabe Ba sabon labari ba ne Farfesa Charles Chukwuma Soludo ne ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra.

Farfesan zai gaji Willie Obiano wanda ya yi shekaru takwas.
 Tsohon gwamnan na CBN ya doke ‘yan takara irinsu; Andy Uba, Ifeanyi Uba da Valentine Ozigbo a zaben. Hakan na nufin APGA ce za ta cigaba da mulkar jihar Anambra.
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments