Sanarwar da hukumar zaben ta fitar, ta ce wadanda aka fitar da sunayen nasu, an yi la’akari da cikakkun bayanan da aka samu daga jam’iyyun siyasar su.
‘Yan takarar shugaban kasa da aka fitar da jerin sunayen nasu sun hada da Asiwanu Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar (APC); Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na Jam’iyyar Labour Party (LP), Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar (NNPP) da Adebayo Adewole na Jam’iyyar (SDP), da sauransu.
Amma APC bata da dan takara a mazabar shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, wato Sanatan Yobe ta Arewa yayin da aka fitar da sunan tsohon Ministan Harkokin Niger Delta Godswill Akpabio a matsayin dan takarar APC na Akwa Ibom a Arewa maso Yamma.
Wani karin bayanin da aka yi a cikin jerin sunayen ya nuna cewa ‘yan takara 1,101 ne ke neman gurbi daga cikin kujeru 109 na majalisar dattawa, yayin da ‘yan takara 3,122 ke neman gurbi daga cikin kujeru 469 a majalisar wakilai.
Daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar, akwai 3,875, wadanda suka kunshi 35 na shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa, 1,008 na majalisar dattawa da 2,832 na majalisar wakilai.
Hakazalika, sunayen mata 381 ne da suka fito takara, abin da ya kunshi daya ta shugaban kasa, 92 na majalisar dattijai, da 288 na majalisar wakilai da ke takara.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya fitar ta ce: “a takaice dai, dukkanin jam’iyyun siyasa 18 sun tsayar da ‘yan takara da abokan takararsu a zaben shugaban kasa.