Daga Walid Hari
A ranar Labarar nan ne ake sa ran kotun ma’aikata da ke Abuja, babban birnin Najeriya za ta yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayyar kasar ta kai kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU.
A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe wata bakwai tana yi.
Ma’aikatar kwadago ta kasar ta ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’in ta ci tura.
Gwamnati tana son kotun ma’aikatan ta bai wa mambobin ASUU umarnin su koma bakin aiki, a yayin da ake ci gaba da shari’a a kan batun.
Tun da fari dai, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen yajin aikin na ASUU.
ASUU ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.