Ministan kiwon lafiya na kasar Ghana Kwaku Agyeman-Manu, ya bayyana cewa, kasarsaa za ta kafa asusun yaki da cutar kanjamau na kasa, don bunkasa shirin takaita tare da kawar da cutar baki daya.
Ministan ya bayyana hakan ne, a jawabi na musamman da ya gabatar, yayin bikin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya da aka gudanar a Accra, babban babban birnin kasar.
Agyeman-Manu yace, shugaban kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, zai kaddamar da asusun nan da kwanaki masu zuwa, a matsayin wani bangare na yunkurin kasar na cimma burin da duniya ke fatan cimma na 95-95-95 nan da shekarar 2030.
Ministan ya kara da cewa, shawarar gwamnati na kafa asusun, tamkar amincewa ne da kalubalen kara cin gajiyar albarkatun kasa, wajen yaki da cutar, don rage ta da kuma kawar da sabbin cututtuka da za su iya bullowa