Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da Samame kan masu tsattsauran ra’ayi a yankin Arewa maso gabashin kasar nan inda tayi nasarar kashe mayakan Boko Haram 11
Mai magana da yawun rundunar Musa Danmadami shine ya bayyana haka a jiya Alhamis, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce da yawa daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram da ISWAP, sun tsere da raunukan harbin bindiga, a samame daban-daban da sojojin suka kaddamar a yankin jihohin Borno da Yobe dake arewa maso gabashin kasar daga ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa daya ga watan Disamba.
Ya kara da cewa, farmakin sojojin, ya kai ga kubutar da wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su daga maboyar ‘yan ta’addan, tare da kame a kalla ‘yan bindiga 47 da masu taimaka musu.
Jami’in ya ce, a ranar 20 ga watan Nuwamba, yayin daya daga cikin irin wadannan kwanton bauna da samame da aka kaddamar, sojojin kasar sun yi nasarar damke wani kasurgumin mai samarwa ‘yan Boko Haram da ISWAP kayayyaki, a wani shingen binciken sojoji da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno da ke yankin arewacin kasar.