Ganduje na shan yabo daga al’ummar Rimin kebe

An yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa waiwayar aikin titin Rimin kebe dake karamar hukumar Ungoggo a jihar kano.

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi

Shugaban matasa kuma dan rajin cigaban yankin Rimin kebe Alhaji Mahmuda Liman Zangon kabo shine yayi wannan yabo a zantawarsa da manema labarai.

Kabo ya bayyana cewa kimanin shekaru takwas kenan da fara aikin titin inda yake rokon gwamnati da ta taimaka ta kammala aikin titin a wannan karo a cikin waadin da aka dauka, dan Samar da walwala ga al’ummar yankin.

Kazalika yace kammala aikin titin zai rage cinkoson ababan hawa a yankin kuma zai bada dama ga mashina masu kafa uku wajan yin zirga zirga ta kaiwa da komowa a yankin.

Ya kuma bukaci al’ummar yankin da su kaucewa zaba shara a magudanun ruwa wanda hakan ka iya haifar da ambaliyar ruwa dan gujewa zaizayar kasa.

Daga karshe ya yabawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa dawo da kasuwanci da walwala a yankin musamman a bakin titin da ake gudanar da aikin sa a yanzu haka.

Editor, A S gwammaja

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments