Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin tana sa lura game da yanayin da ake ciki a kasar Burkina Faso bayan da aka yi juyin mulkin soji a kasar, kana tana son yin kokari tare da sassan kasa da kasa, wajen taimakawa kasar kaiwa ga cimma samun zaman lafiya da bunkasuwa. Mao ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Asabar.
Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta lura da yadda Burkina Faso, ta sanar da ci gaban ta, da bin jadawalin wucin gadi da kungiyar ECOWAS ta cimma daidaito kan sa a baya, tana kuma girmama zaben jama’ar kasar Burkina Faso, da yin imani da cewa, jama’ar kasar za su iya daidaita harkokin cikin