Sashen dake lura da mahakar mai ta Daqing, dake karkashin babban kamfanin albarkatun man fetur na kasar Sin, ya ce kawo yanzu, mahakar danyen mai ta Daqing, ta samar da jimillar danyen mai da yawan sa ya kai sama da tan biliyan 2.4, tun fara aikin ta a shekarar 1959. Mahakar man dai na kan gaba, wajen samar da albarkatun mai a kasar Sin, ta kuma samar da kaso 40 bisa dari, na daukacin albarkatun man da ake hakowa a kasar Sin a tsawon wannan lokaci.
Cikin shekaru sama da 60, mahakar Daqing ta gudanar da aiki ba tsayawa, inda ta taba jera shekaru 27, tana samar da danyen mai da yawan sa ya kai sama da tan miliyan 50 a ko wace shekara. A kuma shekarun baya-bayan nan, adadin mai da iskar gas da take samarwa ya haura kimanin tan miliyan 40 duk shekara.
Mahakar Daqing dai na cikin manyan cibiyoyin hako mai a kasar Sin, tana kuma yankin lardin Heilongjiang, dake arewa maso gabashin kasar Sin. Ta kuma ba da gagarumar gudummawa ga zamanintar da masana’antar sarrafa albarkatun man fetur a kasar Sin. (Saminu Alhassan)