China zata hada hanu da kasar Somalia a wasu fannoni kimiyya

Shugaban kasar China  Xi Jinping ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, a shirye kasar sa take ta ba da taimako gwargwadon karfinta, don sake gina kasar Somaliya, da raya zamantakewar al’umma da tattalin arziki na Somalia.

kuma zata karfafa hadin gwiwar kamfanonin kasashen biyu, da su yi kokarin yin aiki a sassan da suka hada da aikin gona, da kamun kifi da kiwon lafiya.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud. Yana mai cewa, kasar Sin tana goyon bayan gwamnatin Somaliya, wajen kara karfinta na tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta’addanci.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments