Shugabancin kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi ta kasa ya koka dangane da kaidojin da babban bankin kasarnan ya samar na takaita yawan kudaden da zaa fitar a bankuna da cewar hakan zai durkusar da kasuwancin yayanta a kasarnan.
Shugaban kungiyar Alhaji Mustafa Ali ne ya sanar da hakan a zantawarta da manema labarai a ofishinsa dake nan jihar
Mustafa Ali ya koka kan cewar kamata yayi gwamnatin tarayya ta Samar da tsarin da zai ceci yan kasuwa musamman kanana kafin ta aiwatar da wannan sabon tsarin na sauya fasalin kudi ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin kasuwanci a kasarnan.
Ya kuma koka dangane da yadda tsarin kasuwacinsu zai fuskanci kalubale idan har babban bankin kasarnan ya dage akan wadannan sabbin kaidoji da ya bijiro dasu kan cewar mutum daya ba zai cire kudin daya haura naira dubu dari ba daga cikin asusun ajiyarsa na banki ba.
Shugaban ya bayyana cewar kasarnan ba ta Kai munzalin da za tayi amfani da wannan sabon tsarin da ake yiwa lakabi da cashless policy ba kasancewar tsarin tattalin arzikin kasar na cikin mashashshara.
Don Haka. yake kira ga gwamnatin tarayya kan ta gaggauta yin duba na tsanaki kan wannan sabon tsarin da ba zai haifar wa da kasarnan da mai ido ba wanda idan gwamnati bata farga ba zai lalata kasuwancin dubunnan alumma a fadin kasarnan.
Daga karshe yayi kira ga yayan kungiyarsu kan cewar su cigaba da baiwa Shugabancin kungiyar hadin kai da goyon baya kasancewar kungiyar a shirye take wajen kare musu mutuncinsu da kuma kwatar musu yancinsu musamman wadanda ke gudanar da kasuwacinsu a sassa daban daban na jihohin kudancin kasarnan.