Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa, alluran rigakafin COVID-19 guda biyu da kasar Sin ta samar da su, na da tasiri kashi 70 cikin 100, wajen hana kamuwa da cutar mai tsanani ga mutane masu shekaru 60 zuwa sama. Kuma adadin zai iya kaiwa kashi 95 bisa dari bayan karbar allura ta uku dake kara karfin garkuwa.
Kasar Sin mai yawan jama’a miliyan 267 masu shekaru sama da 60, tana hanzarta yiwa wannan rukuni alluran rigakafin cutar.
A karshen watan Nuwamba, kasar Sin ta fitar da wani shirin aiki, don inganta yawan allurar rigakafin a tsakanin tsofaffi. Galibin bukatun da aka gabatar a cikin shirin aikin, ya zuwa yanzu ana gudanar da su a zahiri, tare da kafa tantuna a gyefen hanya da kuma tashoshin yin allurar rigakafin da aka kafa a birane da dama, da kara kaimi wajen wayar da kan tsofaffi kan kiwon lafiya da kara sanya iso kan yanayin lafiyarsu.
A farkon wannan mako ne, gwamnatin kasar Sin ta ba da sanarwar bayar da kashi na biyu na allurar kara garkuwa kan rigakafin COVID-19 ga rukunoni masu rauni wadanda suka karbi alluraa kara karfin garkuwa na farko sama da watanni shida da suka gabata.
A kasar Sin, sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummar kasar an yi musu cikakken rigakafin. Yayin da kusan kashi 87 cikin 100 na mutanen da suka haura shekaru 60, an yi musu cikakkiyar rigakafin.
A cewar masana kiwon lafiya, kowane kashi a wannan rukuni da ya karbi rigakafin, yana nufin kiyaye mutane miliyan 2 da ka iya jawi mutuwa sakamakon cutar.
Kasar ta Sin, ta mayar da hankalinta kan matakan yaki da COVID-19 da shawo kan kamuwa da cutar da kuma magani da nufin hana kamuwa da cutar mai saurin hallaka toff in a kasar.
Rahoton yace Tsofaffi, wadanda ke da raunin garkuwar jiki galibi suna fama da wata cuta, sun fi shiga mummunan yanayi, idan corona ta kama su abin da yasa ake ba su fifikon kariya kenan daga kamuwa da kwayar cuta mai saurin yaduwa