Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi taron gaggawa da manyan jami’an tsaro a Abuja a ranar Litinin.
Wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar a karshen mako, ta ce taron zai mayar da hankali ne kan yadda za a karfafa matakan tsaro a sassan kasar.
Taron zai wakana ne bayan da Amurka ta fitar da wata sanarwa da ke cewa akwai yiwuwar akai hare-hare a wasu sassan kasar, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.