kwanakin nan ne, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin mai yada shirye-shiryen sa akan kasashen Afirka wato CMG Africa, ya gudanar da wasu bukukuwa na musamman kan “Sabon tafarkin kasar Sin da Duniya” a kasashen Kenya da Afirka ta kudu.
A yayin taron tattaunawa ta musannan da ya gudana a kasar Kenya bisa “Sabon tafarkin kasar Sin da duniya”, jakadan kasar Sin dake Kenya Zhou Pingjian, ya tattauna da editoci da ‘yan jaridu sama da 40 daga kasashen Afirka daban-daban.
Jakada Zhou Pingjian ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara samar da gudummawar albarkatu ga hadin gwiwar kasa da kasa, da kokarin cike gibin dake tsakanin arewaci da kudanci, tare da samar da goyon baya da taimako ga kasashe masu tasowa wajen habaka su.
Bugu da kari, an shirya taron karawa juna sani kan “Sabon tafarki na kasar Sin da duniya” a kasar Afirka ta kudu wanda CMG tare da hadin gwiwar jami’ar Johannesburg ta kasar Afirka ta kudu suka dauki nauyin shiryawa tare cikin nasara a birnin Johannesburg. Inda aka gayyaci wakilai da dama daga majalisar dokokin Afirka ta kudu da bangaren gwamnati, da jami’an ilimi domin halartar taron.