An bayyana cewa, akwai yuwuwar farashin makamashi zai ragu da kashi 11.2 cikin 100 a shekarar 2023, bayan da ya karu da kashi 59.1 a wannan shekarar
Bayanin hakan na kunshe ne cikin jawabin da Bankin Duniya ya yi na hasahen farashin makamashi.
Yace makamashin ana sa ran sa ran zai ragu da kashi 11.2 cikin 100 a shekarar 2023, bayan da ya karu da kashi 59.1 a bana.
A cikin rahoton, an bayyana cewa yayin da damuwa game da samun makamashi a cikin watannin hunturu masu zuwa ya karu a Turai, kasuwannin makamashi na fuskantar matsalolin samarwa kuma farashin makamashi zai iya bayana a farashin fiye da yadda ake tsammani a wasu kayayyaki musamman abinci, kuma yana iya tsawaita matsalolin karancin abinci.
Yayin da ake jaddada cewa hauhawar farashin kayayyaki na iya tsawaita, rahoton ya yi nuni da cewa ana sa ran kididdigar farashin makamashi da ta hada da mai da iskar gas da kuma kuza, za ta karu da kashi 59.1 cikin 100 a bana idan aka kwatanta da bara.
A cikin rahoton, an bayyana cewa ana sa ran hasashen farashin makamashi zai ragu da kashi 11.2 cikin 100 a shekarar 2023, amma duk da raguwar, farashin zai ci gaba da kasancewa kashi 75 cikin 100 sama da na matsakaicin shekaru 5 da suka gabata