Babu abin da zai hana raba makarantun mata da na maza: Gwamnatin Bauchi

Daliban makarantun sakandare a halin yanzu suna zanga-zanga a titunan Bauchi kan wata sabuwar doka da gwamnati ta kawo na raba mata da maza a makarantu.

Dalibai sun koma makaranta ne a hukumance yau (Litinin) a sassan jihar kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Mr Aliyu Tilde, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shiri don raba dalibai mata da maza a makarantun jihar.

Za a kaddamar da dokar ne wurin da zai yi wu – Tilde Tilde, a jawabin da ya yi wa manema labarai bayan taron majalisar zartarwa na jihar ya ce za a aiwatar da dokar ne a inda aka ga zai yi wu. An bullo da tsarin ne don inganta tarbiyya.

Ya kara da cewa an bullo da tsarin ne domin magance tabarbarewar tarbiyya da ya zama ruwan dare tsakanin daliban makarantun sakandare.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments