Zamu kula da ‘yan fansho tare da dawo da martabar Ilimi idan mukarabi kafa gwamnati a jihar Kano: Salihu Tanko yakasai

Dan takarar Gwamna a jamiyyar PRP Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta biyan yan fansho hakkokinsu da zarar yayi nasara a babban zaben shekara ta 2023.

Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.

Dan takarar ya bayyana cewar alamarin fansho abu ne da yake bukatar kulawa ta musamman duba da kasancewar maaikaci ya kare rayuwar sa yana aikin gwamnati Wanda da wadannan harkokin nasa ne zai cigaba da tafiyar da alamuran sa har karshen rayuwar sa.

Ya kuma nuna damuwar sa dangane da gwamnatin da ta gabata tayi amfani da kudadensu wajen gine ginen da ba zai amfani yan fansho ba, Sannan gwamnati mai ci ta gaza warware Matsalar Wanda sanadiyar hakan kudaden sukataru ta yadda gwamnatin yanzu take ganin bata da kudaden da zata iya biyansu hakkokinsu.

Yakasai ya kara da cewa idan Allah ya bashi nasara a babban zaben shekara ta 2023 zai zo da sabbin tsare tsaren da ba sai an ciyo basusuka ba don gudanar da wasu ayyukan.

Yace cin bashi ba laifi bane idan zaa yi amfani da kudaden wajen yin ayyukan da Zasu gina alumma, tun da dama daga cikin kasashen duniya ma suna cin bashi ciki har manyan kasashen duniya wanda dashi suke gina alummar su.

Kazalika Ya bayyana cewar idan gwamnati zata kulla yarjejeniya da kamfanoni masu zaman kansu ta kuma Samar musu da yanayi mai kyau Zasu iya Samar da managartan tsare tsare da ayyukan da ba sai gwamnati ta shigo ciki ba, Wanda ba sai gwamnati ta je ta ciyo basusuka ba.

Dangane da tabarbarewar ilimi kuwa dan takarar ya bayyana cewar gyara harkokin ilimi tun daga matakin firamare Wato tushe shi ne zai magance tabarbarewar ilimi a jihar Kano kasancewar bangaren ilimi ba abu ne da zaa taba shi sama samaba kasancewar ba aiki ne da ido zai iya gani ba kamar aikin gadar sama .

Don haka ya ke baiwa alummar jiharnan tabbacin cewar idan har sukayi nasara a babban zaben shekara 2023 Zasu gyara harkokin ilimi tun daga tushe Wanda zai taimaka wa dalibai damar Cin jarabawa har zuwa matakin jamia.

Daga karshe yayi kira ga yayan jamiyyar da jagororinsu kan su saki jikinsu su tunkari alumma su nemi hadin kansu tare da wayar musu da Kai kan cewar Su suke da damar cin zabe a jihar nan Don baiwa masu jini a jika damar jagorancin alumma.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments