An dakatar da koyarwa da yaren turanci a makarantun Firamaren Najeriya.
Wannan ya biyo bayan sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro, wanda ya wajabta koyarwa da yaren uwa a matakin Firamare.
Hakan na nufin, a jihar Kano, da sauran jihohin da Hausa yafi tasiri, yaren zai zama hanyar koyar da darasi a makarantun.
Ministan ilimi, Adamu Adamu, yace daga matakin ƙaramar Sakandire, za’a riƙa haɗawa da turanci wajen bayar da darasin.
Me za ku ce?